Tsaro
AFAN:tayi kira ga gwmanati da ta samarwa manoma tsaro
Kungiyar manoma ta Nijeriya (AFAN) tayi kira ga gwamantin tarayya da ta samar da tsaro da kuma wadata manoman hadi da saukaka farashin taki da sauran kayayyakin noma a kasar nan.
Shugaban kungiyar manoma ta kasa Kabir Ibrahim, ne ya bayyana hakan a zanatwarsa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN.
Wanda ya kara da cewa ‘manoman kasar nan na bukatar a samar musu da kayan aikin na zamani domin samar da wadataccen abinci a fadin kasa’.
Kabir Ibrahim ya kuma kara da cewa ‘rashin tsaro na hana manoma zuwa gonakin su, don hakan akwai bukatar asamar musu da ingantaccen tsaro, da kuma samar da kayayyakin noman na zamani da kuma habaka cibiyoyin noma a fadin kasar za nan.
*
You must be logged in to post a comment Login