Labaran Wasanni
AFCON 2021: Sierra Leone ta gayyaci ‘yan wasa 16
Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Sierra Leone John Keister ya gayyaci ‘yan wasan kasar 16 dake taka leda a kungiyoyi daban-daban a fadin duniya don buga wasan da zasu fafata da Najeriya a mako mai zuwa na neman tikitin gasar cin kofin Afrika na 2021.
Leone Stars dai zasu kara da Super Eagles a ranar Juma’a 13 ga watan Nuwamba a filin wasa na Samuel Ogbemudia dake birnin Benin a jihar Edo, kafin itama ta karbi bakuncin Najeriya bayan kwanaki hudu da kammala wannan wasan.
Leone Stars ta zo ta hudu a rukunin L da maki daya a wasanni biyu, yayin da Super Eagles take kan gaba da maki shida a wasanni biyun farko.
Kuma idan Najeriya ta yi nasara a wasannin biyu kai tsaye zai bata damar samun tikitin zuwa gasar.
AFCON: Najeriya ta gayyaci ‘yan wasa 24
AFCON 2021: Za’ai wasan Najeriya da Sierra Leone ba ‘yan kallo
‘Yan wasan da Keister ya gayyata sun hada da Osman Kakay daga Queens Park Rangers a Ingila da Mustapha Dumbuya daga Tampa Bay Rowdies a Amurka da Alie Sesay daga Zira FK a Azerbaijan da Kwame Queen daga Vikgur Reykjavik a Iceland da Mohamed Medo daga Kamara FC Haka a Finland da Kelvin Wright daga Orebro a Sweden da George Davies daga Austria da Mohamed Turay daga China da kuma Mustapha Bundu daga Belgium.
You must be logged in to post a comment Login