Labaran Wasanni
AFCON 2021: Za’ai wasan Najeriya da Sierra Leone ba ‘yan kallo
Ma’aikatar wasanni ta Najeriya tare da hadin gwiwar kwamitin karta kwana kan cutar Corona da shugaban kasa ya kafa, sun ce za a gudanar da wasan da Najeriya za tayi da Sierra Leone a ranar 13 ga watan Nuwamba na neman tikitin gasar cin kofin Afrika na shekarar 2021 a filin wasa na Samuel Ogbemudia dake a birnin Benin na jihar Edo ba tare da ‘yan kallo ba.
An dai cimma wannan matsayar ne yayin da gwamnatin jihar Edo ke tattauna yiwuwar barin ‘yan kallo su shiga filin wasan don kallo.
Ma’aikatar wasannin na ganin cewa barin ‘yan kallo shiga filin wasan zai jawo a karya doka da ka’idojin hana yaduwar cutar Corona.
A wata wasika da ma’aikatar wasannin ta aike wa mataimakin gwamnan jihar Kwamaret Philip Sha’aibu, na cewa, “Muna so mu ja hankalin ka kan yarjejeniyar da muka kulla da gwamnatin tarayya kafin ta amince a dawo cigaba da harkokin wasanni a kasar nan”.
Daga cikin yarjejeniyar akwai yin gwajin lafiyar kowane dan wasa kafin a fara wasa tare da kauracewa tara taro jama’a masu yawa ta hanyar hana ‘yan kallo shiga filin wasa domin dakile yaduwar cutar Corona.
You must be logged in to post a comment Login