Labaran Wasanni
AFCON 2022: Buhari ya ta ya Super Eagles murnar tsallakawa zuwa wasannin ƙungiyoyi 16
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles murnan nasara a wasannin gasar kofin nahiyar Afrika ta (AFCON) da ke gudana a kasar Kamaru.
Super Eagles dai tayi nasara da ci biyu da nema a kan kasar Guinea Bissau a wasan da suka fafata ranar Laraba 19 ga Janairun 2022.
Mataimaki namusamman ga shugaban kan harkokin ya da labarai Femi Adesina ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Ta cikin sanarwar da ya wallafa ya ce shugaban ya kuma mika sakon godiya ga mai horar da tawagar Austin Eguavoen sakamakon jajircewarsa har Super Eagles ta samu wannan nasara.
“Yana mai cewa nasarar da kungiyar ke samu a bune da zai farantawa ‘yan Najeriya da dama, a don haka ya ke mika godiya tamusamman ga su kansu ‘yan wasan da suke wakiltar Najeriya,”‘
Ya kuma bukaci ‘yan wasan tawagar da su ci gaba da taka rawar gani domin Najeriya ta samu nasarar lashe gasar da ke gudana a kasar ta Kamaru.
Super Eagles dai ta kammala a mataki na farko a rukunin D da maki 9 bayan nasarar wasanni uku da ta buga a gasar ta AFCON wanda tuni ta samu damar kaiwa zagaye na kasashe 16 a gasar.
You must be logged in to post a comment Login