Labaran Wasanni
AFCON 2022: kasar Egypt ta kai wasan karshe bayan doke mai masaukin baki Cameroon
Kasar Masar (Egypt) ta yi nasarar kaiwa wasan karshe a gasar cin kofin Afrika ta AFCON ta shekarar 2022 bayan doke masu masaukin baki kasar Cameroon.
Kamaru dai ta yi rashin nasara da ci 1 da 3 a bugun daga kai sai mai tsaran gida, bayan tinda fari an tashi wasa 0-0.
Fafatawar dai ta gudana a ranar Alhamis 03 ga Fabrairun 2022 a kasar ta Kamaru.
Kasar Kamaru dai itace ke karbar bakuncin gasar, sai dai rashin nasarar datai ya sa bazata lashe gasar ba.
Yayinda kasar Masar zatai yunkurin lashe gasar a karo na 8 a tarihi tin bayan fara gasar.
Wasan karshe dai zai gudana a ranar 06 ga watan da muke ciki tsakanin kasar Senegal wadda bata taba lashe gasar ba a tarihi.
Zuwa yanzu dai kasar Burkina Faso da kuma Kamaru za suyi wasan neman mataki na uku, bayan sunyi rashin nasara a wasannin kusa da karshe a gasar.
You must be logged in to post a comment Login