Labarai
AFCON 2022: Najeriya ta faɗa rukuni na huɗu
Tawagar ƙwallon ƙafa ta Najeriya, Super Eagles ta fada rukuni na huɗu a gasar cin kofin nahiyar Afirka da za’a gudanar a ƙasar Kamaru a shekarar 2022.
Super Eagles wadda ta lashe gasar sau uku, tana rukunin da ya ƙunshi ƙasar Masar da Sudan da kuma Guinea-Bissau.
Mai riƙe da gambun gasar da ta lashe a shekarar 2019 a ƙasar Masar, Algeria tana rukuni na biyar da ya haɗar da SierraLeone da Ivory Coast da kuma Equatorial Guinea.
Mai masaukin baƙi, kasar Kamaru kuwa ta na rukunin farko da ya haɗar da Burkina Faso da Habasha da kuma Cape Verde.
Rukuni na biyu kuwa ya ƙunshi ƙasar Senegal da Zimbabwe da Guinea da kuma Malawi.
Yayin da Rukuni na uku ya hadar da ƙasar Morocco da Ghana da Comoros da kuma ƙasar Gabon.
Rukuni na shida na ƙarshe kuwa ya ƙunshi ƙasar Tunisia da Mali da Mauritania, da kuma Gambia.
Za dai a fara bikin buɗe gasar ne da karawa tsakanin Kamaru da Burkina Faso a ranar 9 ga watan Janairu da ake sa ran karkarewa a ranar 9 ga watan Fabrairun shekarar 2022.
You must be logged in to post a comment Login