Labaran Wasanni
AFCON: Najeriya ta gayyaci ‘yan wasa 24
Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles Gernot Rohr ya gayyaci ‘yan wasa 24 don fafatawa da Sierra Leone a watan Nuwamba mai zuwa a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Afrika ta shekarar 2021.
Super Eagles dai zata hadu da Leone Stars a ranar 13 ga watan Nuwamba a birnin Benin dake jihar Edo kafin itama ta kai masu ziyara a gidansu ranar 17 ga watan na Nuwamba.
‘Yan wasan da Rohr ya gayyata sun hada da Victor Osimhen daga Napoli da Joe Aribo daga Glasgow Rangers Oghenekaro Etebo daga Galatasaray da Emmanuel Dennis daga Club Brugge da kuma mai tsaron gida Daniel Akpeyi daga Kaizer Chiefs.
Sauran ‘yan wasan sune Sebastian Osigwe daga FC Lugano da Kenneth Omeruo da Leon Balogun da Chidozie Awaziem da Alex Iwobi da Moses Simon da Samuel Chukwueze da Chidera Ejuke da Sanusi Zaidu da Kevin Akpoguma da Abdullahi Shehu da Francis Ozoho da Ramon Azeez da Samson Tijjani da kuma Paul Onuachu.
A na bukatar ‘yan wasan su kasance a masaukin da aka tanada masu a birnin Benin ranar 9 ga watan na Nuwamba.
You must be logged in to post a comment Login