Kiwon Lafiya
Afrika tayi bankwana da cutar polio – WHO
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ayyana nahiyar Afurka a matsayin yankin da yayi bankwana da cutar shan inna wato Polio.
A cewar hukumar ta WHO rabuwar nahiyar da cutar ta polio tun a shekarar dubu biyu da goma sha shida.
Hukumar lafiya ta duniyar ta ce, kawo karshen cutar daya ne daga cikin bajinta da aka taba gani a bangaren lafiya a tarihin duniya.
Hakan na cikin wata sanarwa ce da hukumar ta WHO ta fitar a yau talata mai dauke da sa hannun shubagan hukumar, Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus da kuma shugaban kungiyar Rotary International, Holger Knaack.
Sanarwar ta kuma jinjinawa kokarin da ta ce nahiyar afurka ta yi da kuma dukkannin wadanda suka ba da gudunmawa wajen ganin an dakile cutar.
You must be logged in to post a comment Login