Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An kara samun masu Corona a kungiyar mu – Marseille

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Marseille dake kasar faransa ta ce an samu karin ‘yan wasa guda uku da suka kamu da annobar cutar Corona, bayan mutun biyar da aka samu a makon da ya gabata.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar ga manema labarai a yau Talata.

Haka kuma, kungiyar ta ce an dage gasar ta League 1 ta kasar Faransa da aka dauki niyyar farawa a ranar Juma’ar da ta wuce sakamakon ‘yan wasan guda biyar da suka kamu da cutar ta COVID-19.

Marseille ta kuma ce, tuni ta sanar da masu ruwa da tsaki wajen shirya gasar ta League 1, sakamakon samun karuwar mutane uku da suka kamu da cutar bayan da mutune biyar na farko suka kamu, domin samun mafita daga lamarin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!