Labarai
Aikin zaɓe ba zai tafi yadda ya kamata ba, sai da haɗin gwiwar ƙungiyoyin sufuri – INEC
Hukumar Zabe mai zaman kanta ta ƙasa INEC da kungiyoyin sufurin ababen hawa sun gudanar da taro don yin bitar yarjejeniyar fahimtar juna da suka rattaba hannu a zaben 2019 da ya gabata.
Kungiyoyin su ne kungiyar ma’aikatan sufuri ta kasa NURTW da kungiyar masu motocin dakon kaya NATO.
Rahotanni sun bayyana cewa taron ya mayar da hankali don sake nazarin aiwatar da yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin hukumar INEC da kungiyoyin, gabanin zaben gwamnan Anambra da babban zaben 2023 da yake ƙarayowa.
Farfesa Okechukwu Ibeanu, kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin gudanar da zabe ya ce, hadin gwiwa da kungiyoyin biyu wani bangare ne na kokarin tabbatar da sahihin zabe.
Yayin da yake yabon haɗin gwiwa da ƙungiyoyin sufuri Ibeanu ya ce, babu yadda za a yi INEC ta isar da kayan zaɓe yadda ya kamata a dukkan rumfunan zaɓe ba tare da haɗin gwiwar ƙungiyar ba.
A don haka ya bukace su da su yi aiki mai kyau a babban zaben 2023.
You must be logged in to post a comment Login