Labarai
Gwamnatin Sokoto ta tabbatar da mutuwar yara 33 sakamakon cutar Sankarau

Gwamnatin Jihar Sokoto ta tabbatar da mutuwar yara 33 sakamakon barkewar cutar sankarau mai kashe kwakwalwa da aka samu a wasu sassan jihar.
Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Faruk Abubakar, ne ya bayyana hakan a jiya Laraba yayin wani taron wayar da kai da aka gudanar da hakimai kan batun tsaron
A cewar kwamishinan, an samu mutane 256 da ake zargin sun kamu da cutar a kananan hukumomi takwas tun bayan sake bullar cutar kimanin wata guda da ya gabata.
Ya ce karamar hukumar Sabon Birni ce ke kan gaba da mutane 63, sai Wamakko ke da 60, Shagari 51, Tambuwal 33 da Dange Shuni 26
Haka kuma Kebbe ta samu mutane 16, yayin da Bodinga, Gada da Kware suka samu mutane biyu.
You must be logged in to post a comment Login