Labarai
AKTH ya samu nasarar gudanar da aikin kwakwalwa karo na biyu
Asibitin koyarwa na malam Aminu Kano ya gudanar da aikin kwakwalwa karo na biyu inda suka cire wani tsiro tare da samun nassara gudanar da wannan aiki.
Jaridar Kano Focus ta rawaito cewar aikin wanda aka gudanar da shi a asibitin dai an samu nasarar cire wani tsiro ne a jiki malama Nafisa Yusuf ‘yar shekara 47 da haihuwa , kuma ‘yar asalin jihar Edo
Malama Nafisa dai an mai do da ita asibitin na malam Aminu Kano ne bayan ta bi wasu matakai a asibitin koyarwa dake jihar Lagos .
Aikin dai an shafe kimanin awanni biyar ana gudanar da shi, inda ya dauke tarin wasu kwararrun likitoci , daga fanonin daban-daban ne suka gudanar da aikin.
Dr Musbahu Haruna Ahmad , wanda shine babban likitan tiyata na fannin kwakwalwa shi ya jagoranci aikin, ya ce sun sami nasarar aikin ne da taimakon wasu kwararrun a fannoni daban-daban.
Ya kara da cewa sun gudanar da shi a tsanaki ta hanyar sanya wani na’ura ta hancin mara lafiyar ta shiga ta cikin kwakwalwarta har ya kai ga inda ake so ya je .
Shima Dr Ahmed ya kara da cewa a wajen aikin sun yi amfani da wasu kamarori masu kama da abin hangen nisa da wani hasken fitila wanda ya taimaka wa na’urar da aka jura ta hanci nuna inda wannan kari’ yak e tare da ciro shi ta hanci.
Ya kara da cewa mara lafiya Nafisa tuni aka sallame ta bayan da aka tabbatar da ta shafe kwanaki 6 tana kwance a asbiti bayan kamala gudanar da aikin.