Labarai
Akwai bukatar bada tazarar haihuwa domin inganta tarbiyyar yara -Raliya Zubairu
Akwai bukatar bada tazarar haihuwa domin inganta tarbiyyar yara -Raliya Zubairu
Wata malama a sashen tarihi na kwalejin ilimi ta Sa’adatu Rimi dake nan Kano, ta bayyana cewa akwai bukatar bada tazarar hai-huwa ga mata domin samun damar kula da sauran yara, Malama Raliya ta bayyana hakanne jim kadan bayan kammala shirin In Baku na yau jumu’a a tashar Freedom Radio.
Malama Raliya ta kara da cewa “idan mace tana haihuwar ‘ya’ya daya biyu uku, hudu, kuma miji ya sakar mata nauyinsu itace shayarwa, tufatarwa da makaranta, itace asibiti, to don me zata yita haihuwa koda yaushe? Ai sai ta dakata ta rikesu wanda suke hannunta tayi duk abinda zatayi ta inganta rayuwarsu, ni bance ta kashe aurenta ba, idan sun dai-daita sai ta cigaba”.
Shin ko yaya kuke kallon wannan batu?