Labarai
akwai karancin kwararrun akantoci a najeriya-ICAN
Cibiyar horas da kwararrun Akantoci ta najeriya ICAN, ta bayyana cewa duk da yawan ma’aikatan Akanta da kasar nan ke da su, amma har yanzu akwai karancin kwararru a fannin aikin na Akanta.
Shugaban cibiyar ta ICAN Malam Isma’ila Muhammad Zakari ne ya bayyana hakan a jiya ta cikin shirin ‘Mu Leka Mu Gano na nan Freedom Rediyo.
Malam Isma’ila Muhammad Zakari, ya ce komai nisan matakin da mutum ya kai a fannin aikin Akanta matukar bai halarci cibiyar ta su ya yi karatu sannan ya kuma samu nasarar jarabawa ba, to bai zama kwararre ba.
Haka zalika ya kara da cewa tsananin da jarrabawar ke da shi ne ke sanyawa wasu daga cikin masu neman kwarewar ke ganin akwai wahala, wanda suna yin hakan ne don gudun yaye bara-gurbin ma’aikata.
Isma’ila Muhammad Zakari, ya kuma bukaci gwamnatin Jihar Kano da ta samar da fili da cibiyar za ta gina Makaranta don samarwa daliban Kano guraben karatu.
Ya kuma ce duk da ba su taba karbar wani korafi ko zargin almundahana kan wani daga cikin wadanda su ka horas ba, amma dai cibiyar ta yi tanadin dokoki da hukunci mai tsauri kan duk wani kwararren Akanta da aka kama da irin wannan laifi.