Labarai
Za a samu ɗaukewar ruwan famfo a wasu sassan birnin Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da cewa akwai yiwuwar za a samu ɗaukewar ruwan famfo a wasu sassan birnin Kano sakamakon gyare-gyaren da ake yi kan layin wutar lantarki da ke samar wa Matatar Ruwa ta Challawa wuta.
Wannan na cikin sanarwar da Kwamishinan Albarkatun Ruwa, na Jihar Kano, Dr. Dahir M. Hashim, ya fitar.
Sanarwar ta bayyana cewa Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na KEDCO na gudanar da gyaran layin wutar Challawa, yayin da kuma ake gyaran injinan wutar da ake amfani da su a matatar ruwan.
Gwamnatin ta ce za a dawo da samar da ruwan famfo yadda aka saba da zarar an maido da wutar lantarki da kuma kammala gyare-gyaren da ake yi.
You must be logged in to post a comment Login