Connect with us

Labarai

Najeriya na shirin hadin gwiwa da China domin magance matsalar tsaro

Published

on

Jakadan Najeriya a ƙasar China, Janar Abdurrahman Bello Dambazau mai ritaya, ya ce Najeriya na tattaunawa da gwamnatin China domin samun haɗin gwiwa wajen amfani da fasahohin zamani da za su taimaka wajen magance matsalolin tsaro da ke addabar ƙasar.

Janar Dambazau ya bayyana hakan ne a wata hira da sashin Hausa na RFI, inda ya ce a cikin wannan makon Babban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Ambasada Ahmed Umar Guloma, ya jagoranci wata tawaga zuwa China domin gudanar da tattaunawa kan batutuwan tsaro da suka shafi Najeriya da yankin Sahel.

Ya ce matsalar tsaron Najeriya ta shafi ƙasashen makwabta, musamman yankin Sahel da Tafkin Chadi, inda ya bayyana cewa yaɗuwar makamai ba bisa ƙa’ida ba da kuma amfani da miyagun ƙwayoyi na daga cikin abubuwan da ke ƙara rura wutar rashin tsaro.

Jakadan ya ƙara da cewa China na da ingantattun fasahohin sa ido da kayan aikin tsaro da za su taimaka wajen gano maboyar ‘yan ta’adda da kuma kai ɗauki cikin gaggawa. Ya ce tattaunawar da ake yi ta kuma haɗa da batun sayen kayan aikin soja da horas da dakarun Najeriya domin ƙarfafa yaƙi da ta’addanci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!