Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta dakatar da Manajan cibiyar samar da ruwan sha ta Thomas

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da Manajan Cibiyar Samar da Ruwa ta Thomas Regional Water Scheme bayan gano yadda aka lalata tare da sace muhimman kayan aikin cibiyar. Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ya bayyana hakan yayin wata ziyarar duba ayyukan gyaran cibiyoyin samar da ruwa a jihar.

A cewarsa, binciken da aka gudanar ya nuna cewa cibiyar ta daina aiki kusan shekaru uku da suka gabata, inda aka sace kusan dukkan wayoyin lantarki da ke haɗa injinan cibiyar, har ma da wani sabon aikin wutar lantarki da aka kammala watanni uku da suka gabata amma ba a ƙaddamar da shi ba. Ya kuma ce an gano jami’an tsaron da aka ɗora wa alhakin kare cibiyar sun mayar da filinta gona, lamarin da ya sa aka dakatar da manajan domin gudanar da bincike.

Kwamishinan ya ce gwamnatin jihar na ci gaba da gyaran cibiyoyin samar da ruwa a faɗin Kano, tare da jaddada cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya amince a samar da duk kuɗaɗen da ake buƙata domin dawo da su bakin aiki. Ya kuma yi kira ga al’umma su taimaka wajen kare kadarorin gwamnati domin tabbatar da dorewar samar da ruwan sha.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!