Connect with us

Ƙetare

Mojtaba Khamenei ya sha alwashin ɗaukar fansa kan kisan mahaifinsa

Published

on

Sabon jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei, ya sha alwashin ɗaukar fansar kisan mahaifinsa Ali Khamenei, wanda ya mutu a hare-haren Isra’ila da Amurka a ranar farko ta yaƙin.

A wani saƙo da aka wallafa da sunansa domin gode wa waɗanda suka halarci jana’izar mahaifinsa, Mojtaba Khamenei ya ce za su ɗauki fansar jininsa da kuma na sauran waɗanda suka mutu a harin da Amurka da Isra’ila suka kai wanda ya bayyana a matsayin kisan gilla.

Ya kuma jaddada cewa ɗaukar wannan fansa buri ne na al’ummar Iran, yana mai cewa dole ne a tabbatar an aiwatar da ita ba tare da gazawa ba.

Tun bayan da aka ce ya maye gurbin mahaifinsa a matsayin jagoran Iran, Mojtaba Khamenei bai bayyana a bainar jama’a ba, kuma har yanzu ba a ji saƙon murya ko na bidiyo daga gare shi ba, sai dai rubuce-rubucen da ake wallafawa da sunansa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!