Labarai
Alƙalan Kotun Ƙoli da ta ɗaukaka ƙara sun horas da lauyoyi a taron buɗe Ofishin Nureini Jimoh

Ofishin ƙwararren lauya Barista Nureini Jimoh SAN, da ke Kano, ya gudanar da taron bita ga ma’aikatan shari’a da kuma lauyoyi domin ƙara inganta aikin lauya da kuma harkokin shari’a.
Taron wanda ya gudana a ranar Asabar, y haɗa masana da dama a fannonin na aikin lauya da kuma fannin shari’a.
Haka kuma, taron ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin tsohon Alƙalin kotun Ƙoli Mai shari’a Abdu Aboki.
Da ya ke gabatar da muƙala yayin taron, guda daga cikin Alƙalan Kotun Ƙolin Najeriya, Mai shari’a Tijjani Abubakar, ya bayyana buƙatar manyan lauyoyi su riƙa taimaka wa ƙanana da horo da kuma hanyoyin da za su ƙara inganta ayyukansu, musamman ta hanyar fasahar sadarwa da kuma fasahar AI.
Haka kuma, Mai shari’a Tijjani Abubakar ya kuma buƙaci da a ƙara samun haɗin gwiwa mai ƙarfi tsakanin Ƙungiyar Lauyoyin ƙasar nan NBA, Makarantar koyar da aiki Lauya Nigerian Law School da sauran masu ruwa da tsaki, domin tinkarar ƙalubalen da ke ake fuskanta a fannin aikin shari’a.
Shi ma Mai shari’a Habeeb A.O Abiru na kotun ƙoli, ya gabatar da tasa muƙalar yayin taron, yayin da ita ma mai shari’a Olasumbo Goodluck ta kotun ɗaukaka ƙara ma ta gabatar da tata muƙalar, wadda a ciki ta zayyano wasu matsaloli da ke damun fannin shari’a tare da hanyoyin da za a bi wajen magance su.
A ganawarsa da manema labarai, Barista Nureini Jimoh SAN, ya sha alwashin ci gaba da shirya irin waɗannan taruka domin taimaka wa lauyoyi kan yadda za su samu ƙarin ƙwarewa.
Ya ƙara da cewa, “Mun shirya wannan taro ne a wani ɓangare na murnar bikin auren ƴata ta biyu da kuma bikin buɗe sabon ofishina”.
“Dama tun a baya muna shirya taron bita ga lauyoyi, amma yanzu ne muka ƙara ƙarfafa shi, kuma za mu ci gaba da shirya irin wannan taro.”
Shi ma guda daga cikin mahalarta taron Barista Abdul Adamu Fagge SAN, ya gabatar da bukatar ganin alƙalai su na bai wa lauyoyi damar yin amfani da na’urar Kwamfuta ko wayar hannu wajen gabatar da hujjoji yayin gudanar da shari’a,
Taron, ya samu halartar alƙala biyu daga koli watau Mai shari’a Tijjani Abubakar da mai shari’a Habeeb A.O Abiru da kuma Mai shari’a Olasumbo Goodluck daga kotun ɗaukaka ƙara, sai wakilai daga kotunnan Kano har ma da lauyoyi da dama.
You must be logged in to post a comment Login