Labarai
Alƙali-alkalai ta yi gargaɗi kan yin hukunce-hukunce masu cin karo da juna

Alƙali-alkalan Najeroya Mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta gargaɗi alƙalai, da su guji yin amfani da kotu wajen neman hukuncin da ya dace da muradun wasu.
Haka kuma, ta umarce su da su kauce wa ɓoye shari’o’in da suka danganci juna da kuma bayar da umarnin kotu masu karo da juna gabanin zaɓen shekarar 2027.
Mai Shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta bayyana hakan ne a Abuja, yayin buɗe taron shugabannin kotuna na shekarar 2026, wanda Cibiyar Horar da Ma’aikatan Shari’a NJI ta shirya.
Ta ce, ya kamata alƙalai su gudanar da ayyukansu cikin adalci, ba tare da matsin lamba daga ’yan siyasa ko ra’ayin jama’a ya shafi hukuncinsu ba.
You must be logged in to post a comment Login