Connect with us

Labarai

Masar za ta tura wa Saudia tallafin sojoji don kare ta daga hare-haren Houthi

Published

on

Majalisar dokokin Masar ta amince da tura tallafin soji zuwa Saudiyya domin taimaka mata wajen kare kanta daga hare-haren ‘yan tawayen Houthi.

 

Matakin, wanda ya biyo bayan buƙatar da Shugaban Masar, Abdel Fattah al-Sisi, ya gabatar, na iya sanya Masar shiga kai tsaye cikin rikicin yankin, wanda ake yi tsakanin masarautar Saudiyya da ‘yan tawayen Houthi na Yemen masu samun goyon bayan Iran, waɗanda hare-haren da suke ci gaba da kai wa ke barazana ga muhimmiyar mashigar ruwa ta Bab el-Mandeb.

Yayin wata ziyara da ya kai Alkahira, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce yana da matukar muhimmanci a dakatar ta’azzarar rikici a Gabas ta Tsakiya, musamman a daidai lokacin da Amurka da Iran ke ci gaba da yi wa juna barazana.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!