Labarai
Amnesty ta yi Allah wadai da kisan Sheikh Yahaya Masussuka

Ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta yi Allah wadai da kisan fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahaya Masussuka, wanda wasu ’yan bindiga da ke kan babura suka kashe a garin Dutsin-Ma, Jihar Katsina.
Amnesty International ta buƙaci hukumomin Najeriya su gudanar da cikakken bincike cikin gaggawa tare da tabbatar da cewa an gurfanar da duk waɗanda ake zargi da hannu a kisan a gaban shari’a.
Ƙungiyar ta bayyana cewa Sheikh Yahaya Masussuka ya shahara wajen amfani da wa’azinsa wajen ƙarfafa haɗin kai, zaman lafiya, zaman tare tsakanin mabiya addinai daban-daban da fahimtar juna tsakanin Musulmi.
You must be logged in to post a comment Login