Labarai
ALGON ta ja kunne kwamitin karbar mulkin Abba Kabir da ya daina tsoma baki ga mulkin gwamnati mai ci
Kungiyar shugabannin kananan hukumomin jihar Kano 44 ALGON, ta gargadi kwamitin karbar mulki na zababben gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ya daina yunkurin tsoma baki cikin lamuran gudanar da sha’anin mulkin gwamnati mai ci.
Kungiyar ta ALGON ta yi gargadin ne cikin wata sanarwa da shugabanta Muhammad Baffa Takai ya fitar.
A cewar sanarwar, ‘zababben gwamnan Engr Abba Kabir Yusuf na yin azarbabi da shishshigi wajen yunkurin tsoma musu baki wajen lamarin aiwatar da mulkinsu, kamar yadda dokar kasa ta basu a matsayin su na zababbun shugabanin da al’umma suka damka ragamar jagoranci a hannunsu.
A don haka kungiyar ta ALGON ta shawarci shugaban kwamitin karbar mulki na zababben shugaban Jihar Kano Abba Kabir Yusuf da ya dainar yunkurin karya doka wajen fitar da sanarwar zargin da suke yi don gudun kawo tarnaki da zaman lafiya ga harkokin tsaro a Jihar Kano.
Wannan dai na zuwa ne kwana guda bayan da shugaban kwamitin karbar mulki na zababben gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya shawarci shugaban kananann hukumomin Kano 44 da su guji amfani da kudin talakawa, don hada-hadar siyaysa yayin zaben cike gurbin ‘yan majilisu da za’ayi a ranar 15 ga watan Afrilun da muke ciki.
Wannan dai itace dai shawara ta uku da zababben gwamnan Jihar Kano ABBA Kabir Yusuf ya bayar kan harkokin gwamnati gabanin hawansa karagar mulki.
Rahoton: Ummulkhairi Rabi’u Yusuf
You must be logged in to post a comment Login