Labaran Wasanni
All Star Sheka ta doke Ajax Dawakin Kudu a wasan sada zuminci

Kungiyar kwallon kafa ta All Star Sheka ta doke kungiyar kwallon kafa ta Ajax Dawakin Kudu a wasan sada zuminci da suka buga a jiya Litinin 13 ga watan Satumbar shekarar 2021.
Kungiyar ta All Star Sheka, ta samu nasara kan Ajax Dawakin Kudu da ci 1-0 a wasan.
Dan wasan kungiyar ta All Star Sheka Bahago ne ya zura kwallon data bawa kungiyar nasara a mintina na 75 da fara wasan.
An dai buga wasan ne a karamin filin wasa na Dawakin Kudu
You must be logged in to post a comment Login