Labarai
Allah ya yi wa Malam Nata’ala rasuwa

Allah ya yi wa fitaccen jarumin Kannywood din nan Mato Na Mato, wanda aka fi sani da Malam Nata’ala a cikin shiri mai dogon zango na Dadin Kowa rasuwa.
Fitacciyar marubuciya Fauziyya D. Sulaiman ce ta sanar da rasuwar tasa ta cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook a daren Lahadin nan.
Sanarwar ta bayyana cewa “Innalillahi wa’inna ilaihi rajiun, yanzu muke samun labarin rasuwar Malam Nata’ala, Allah Ya gafarta masa, Allah Ya sa jinya ta zama kaffara.”
Jarumin ya jima a kwance yana fama da rashin lafiya, inda ya sha fitowa a cikin wasu faifan bidiyo yana neman taimakon jama’a kan rashin lafiyar da ya ke fama da ita.
Gwamnatin Jihar Yobe ta ɗauki nauyin yi wa marigayin magani, bayan da marigayin ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa shugaban ƙasar Nijar, ya taimaka masa da kuɗi kimanin Naira miliyan 27 domin ya ci gaba da neman magani, bayan ya nemi taimakon jama’ar gari.
Rahotonni sun bayyana chew marigayi Mato Na Mato, wanda aka fi sani da Malam Nata’ala, ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin maidugurin jihar Borno.
You must be logged in to post a comment Login