Connect with us

Labarai

Sallah Idi :  Musulamai su koma kan tafarkin tsira

Published

on

Masallacin Dakata Malam Salisu Khalid Na’ibi , ya ja hankalin Al’ummar Musulmi kan komawa bisa turbar ma’aiki Salallahu Alaihi wasallam wanda Ubangiji ya umarta kasancewar shine hanyar samun tsira da dacewa.

Malam Salisu Khalid Na’ibi, ya yi kiran ne a hudubar sa da ya gabatar yau Jim kadan bayan kammala Sallar Babbar Idi, wacce ta gudana a  Masallacin dake unguwar Dakata.

Na’ibin ya ce duk lokacin da al’umma ta kaucewa umarnin ubangiji, ana jarabtar ta da Annoba wacce hakan na nufin su gyara halayen su tare da kyautata mu’amala kana da komawa ga Allah madaukakin Sarki, bisa yin addu’oi don samun Rahamar sa bisa jagorori na gari.

A nasa jawabin Dagacin Kawaji Alhaji Umaru Adamu, ya yi kira ga al’umma da su bi dukkan ka’idoji da hukumomi suka gindaya na daukan matakan lafiya akan Annobar Cutar Corona, tare kai rahoton duk wani yanayi da basu aminta dashi ba ga hukumomi don kar bata gari suyi amfani da damar wajen cutar da jama’a.

Dumbin al’ummar dake yankin na Dakata da makwabtan ta suka halarci Sallar Idin a Babban Masallacin wanda Na’ibin Masallacin ya yanka Ragon sa na Layya , bayan kammala huduba da Karfe 9 saura na safiyar yau.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,907 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!