Connect with us

Addini

Al’umma su lazimci yin addu’o’I da taimakawa marasashi – Dakta Aliyu Yunus

Published

on

Limamin Masallacin Juma’a na Usman Bn Affan dake kofar Gadan Kaya cikin karamar hukumar Gwale nan Kano, Dakta Aliyu Yunus, ya ce annoba gaskiya ce domin kuwa Annabi Muhammad SAW ya tabbatar da Matsayin annoba a cikin hadisi.

Dakta Aliyu Yunus ya bayyana haka ne jimkalan bayan kammala Hudubar sallar juma’a daya gabatar a Masallacin dake kofar Gadan kaya.

Limamin ya kuma ce akwai abubuwa da dama da musulmi ya kamata su lizimta musamman addu’o’i da taimakon marasa galihu dake cikin al’umma.

Dakta Aliyu Yunus ya ce hukumar Masallacin ta hada kai da jami’an Kula da Masallacin damin ganin al’umma sun bi dukkan ka’idojin da Gwamnatin Kano ta bayar domin kaucewa kamuwa daga annobar Covid 19.

Wakilin mu Bilal Nasidi Mu’azu ya ruwaito cewa masallata da dama sun sanya takunkumin rufe baki da hanci,inda Masallacin ya samar da sunadarin wanke hannu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 332,988 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!