Labarai
Yan Najeriya sun kalubalanci kotu kan korar karar da wata yar sanda ta shigar
Wannan furucin ya biyo bayan korar karar da kotun ma’aikatan ta kora na jami’ar ‘yan Sandan data shigar na korarta da akayi, don tana dauke da juna biyu ba tare da aureba.
mutane na ganin hukuncin zai rage wariyar da bambance-bambancen da ake samu a cikin al’umma.
Al’ummar Nijeriya na cigaba da mahawara tare da bayyana mabambantan ra’ayoyinsu dangane da matakin wata kotun kula da hakkin ma’aikata na yin watsi da hukuncin korar Yan sanda Mata da suka samu juna biyu ba tare da aure ba.
Wadanda suka ce hakan tamkar nuna wariya ne ga ‘yan sanda Mata.
Wannan hukuncin dai ya biyo bayan karar da wata jami’ar ‘yar sanda ta shigar gaban kotun, bayan da rundunar ‘yan sandan kasar nan ta kore ta daga aiki sakamakon samun juna biyu ba tare da aure ba.
Wasu cikin al’umma dai na ganin wannan hukunci zai rage bambance-bambance da ake samu tsakanin Yan sanda mata da maza.
Yayin da a hannu guda kuma wasu ke ganin hakan zai bude kofofin barna ga wadanda ke aikin tabbatar da ‘da’a a tsakanin al’umma.
RAHOTO: Abdulkadir Haladu Kiyawa
You must be logged in to post a comment Login