Labarai
Ambaliyar ruwa ta jefa dubban mazauna Jihar Yobe cikin mawuyacin hali

Ambaliyar ruwa da guguwa mai ƙarfi sun jefa dubban mazauna Jihar Yobe cikin mawuyacin hali, inda mutane 34,533 daga iyalai 9,845 suka fuskanci matsalar a ƙananan hukumomi 15 na jihar.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta Jihar Yobe, YOSEMA, ta ce mutane 11 sun rasa rayukansu, yayin da wasu 303 suka samu raunuka tun daga ranar 8 ga watan Mayu zuwa 10 ga watan Agustan 2026.
Rahoton hukumar ya kuma bayyana cewa gidaje da ɗakuna sama da 21,000 sun lalace ko kuma suka ruguje, lamarin da ya tilasta wa mutane 1,120 barin gidajensu domin neman mafaka.
Karamar hukumar Karasuwa ce ta fi fama da iftila’in, inda mutane dubu 3,288 abin ya shafa.
A babban birnin jihar Damaturu ambaliyar ta shafi mutane 1,554 tare da haddasa mutuwar mutum guda.
You must be logged in to post a comment Login