Labarai
Sojoji sun kama abubuwan fashewa guda 180 a jihar Zamfara

Dakarun hadin gwiwar rundunar Operation fansar yamma sun kama wasu abubuwan fashewa guda 180 da ake zargin ana safarar su zuwa hannun ’yan ta’adda a jihar Zamfara.
Hakan dai na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar Laftanar Kanal Aliyu Danja ya fitar a yau Asabar.
Ya ce dakarun sun kuma kashe ’yan ta’adda biyu a wasu samame daban-daban da suka gudanar a jihar.
Ya ce a ranar Juma’a, 14 ga Agusta, dakarun Soji 2 sun kama wani mai safarar makamai da abubuwan fashewa yayin binciken ababen hawa.
Kazalika ya bukaci al’umma da su dinga sanar da jami’an tsaro duk wani motsin da ba su aminta da shi ba
You must be logged in to post a comment Login