Jigawa
Ambaliyar ruwa : Mutane 23 sun rasa rayuka a jihar Jigawa
Kimanin mutane 23 ne suka mutu a sanadiyar ambaliyar ruwa da ta faru a kananan hukumomin jihar Jigawa 24 da sauyawa iyalai sama da dubu hamsin matsugunan su.
Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Yusuf Babura ne ya tababtar da hakan, inda ya ce galibin wadanda suka rasun kananan yara ne.
Babura na cewa rushewar gine-gine sanadiyar mamakon ruwan sama na daga cikin dalilan da suka sabbaba mutuwar mutanen.
Rahotanni na nuni da cewa, an samu mutuwar mutane hudu a Gwaram da uku a Babura da Ringim da Malam Madori da kuma wasu biyu a Birnin Kudu da Guri.
Shugaban hukumar ya kara da cewa ambaliyar ruwan ta shafi kananan hukumomi 24 cikin 27 na jihar ta Jigawa, banda kananan hukumomi 17 da lamarin ya fi yin kamari.
You must be logged in to post a comment Login