Labarai
Ambaliyar ruwa na ci gaba da mamayar jihar Bauchi

Maimartaba Sarkin Bauchi Dr. Lirawanu Sulaiman Adamu ya yi kira ga masu hannu da shuni da su tallafawa waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar.
Sarkin ya bayyana hakan ne, yayin da ya ziyarci sansanin waɗanda ambaliyar ruwa ta raba da gidajen su.
Hukumomi a jihar, sun tabbatar da rasuwar mutane 8 sanadiyyar ambaliyar tare da asarar dukiya ta sama da miliyan ɗari biyu.
Ambaliyar dai ta fi ƙamari a wasu yankunan na ƙaramar hukumar Kirfi.
You must be logged in to post a comment Login