Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Ambaliyar ruwa ta hallaka mutane 7 da lalata gidaje fiye da 2000 a jihar Jigawa

Published

on

Majalisar karamar hukumar Ringim da ke jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar mutane bakwai sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ya rutsa da su, yayinda gidaje sama da 2,000 suka lalace hadi da gonaki.

Shugaban karamar hukumar ta Ringim Abdulrashid Ibrahim ne ya tabbatar da hakan yayin zantawar sa da manema labarai a yau, lokacin da ya kai ziyara yankunan da ambaliyar ruwan ya auku, don jajanta wa wadanda ibtila’in ya rutsa da su.

Haka kuma ya bayyana cewa akwai bukatar kai agajin gaggawa a yankunan da suka fuskanci matsalar ambaliyar ruwan, tare da cewa wannan shi ne karo na farko da suka fuskanci hakan, tun bayan wanda ya faru a shekarar 2003.

Rahotanni sun bayyana cewa Sama da hekta 100 na gonaki ne suka lalace, hadi da amfanin gona, inda manoma sama da 45 da kuma iyalan su suka rasa matsugunan su.

A cewar shugaban karamar hukumar ta Ringim mutanen sun rasa rayukan na su ne a dai-dai lokacin da suke kokarin ficewa daga yankunan su a kwale-kwale, inda kwale-kwalen ya kife da su a cikin ruwa, lamarin da ya yi sanadiyyar asarar rayukan su.

Rahotanni sun ruwaito cewa daga cikin yankunan da suka fuskanci ambaliyar ruwan akwai Dabi, Auramo, Yakasawa, Algama, Laura, Kayi hawa, Dingare, Siyanku, Nsukum, zangon kanya, Malamawan Yandutse, Kyarama, Sintilmawa , Yan-dutse da kuma Chai-chai Sabuwa.

Abdulrashid Ibrahim ya kuma bukaci gwamnatin jihar da kuma hukumar bada agajin gaggawa ta jiharJigawa da su kai daukin gaggawa zuwa yankunan da suka fuskanci ibtali’in ambaliyar ruwan, kasancewar suna bukatar agajin gaggawa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!