Labarai
Yawan amfani da bayanai ga ma’aikatu zai kawo cigaba a Nijeriya- CITAD
Cibiyar bunkasa fasahar sadarwa da ci gaban al’umma a Kano CITAD, ta bukaci gwamnatin tarraya da ta kara zaburar da ma’aikatu da hukumomin kasar nan da su ringa amfani da bayanai akai-akai wajen gudanar da ayyukansu da ciyar da su gaba.
Shugaban cibiyar Alhaji Zakari Yau ne ya bayyana hakan a taron manema labarai wadda ya gudanar jiya a nan Kano.
A cewarsa, ‘bayanai na taka muhimmiyar rawa wajen gudanar ayyuka musamman a zamanance’.
Ya kuma ce, ‘a wani rahoto da cibiyar gudanar ayyuka ta duniya ta fitar ya nuna cewa, kasashen Afirka da dama ciki kuwa har da Nijeriya na fama da matsalar rashin amfani da bayanai yadda ya kamata wajen gudanar da aiki’.
Freedom Radio ta ruwaito cewa, cibiyar ta kuma ja hankulan gwamnatoci a dukkannin matakai da su kasance masu kiyaye bayanai duba da muhimmancinsu.
You must be logged in to post a comment Login