Labarai
Amfani da hanyar noman zamani ne zai kawo wadatar abinci – Masani
Masana a fannin tattalin arziƙi sun ce amfani da salon noma na zamani zai taimaka wajen samar da abinci.
Malam Mahmud Hamisu Shika na kwalejin fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zariya ne ya bayyana hakan ga Freedom Radio.
A cewar sa, tilas a yi amfani da salon noma na zamani wajen ganin an samar da wadataccen abinci ga ƙasa.
Shika ya ce, “akwai buƙatar samarwa da manoma iri da injinan sarrafa amfanin gona, da maganin feshi”.
Malam Shika ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya kan ta faɗaɗa shirinta na bunƙasa noma zuwa kan Masara, Dawa da Gero da sauransu.
You must be logged in to post a comment Login