Labarai
Amfani da Soshiyal Midiya ya sanya an tsare jami’in soja
Rundunar sojin ruwan ƙasar nan ta musanta rahoton ɓatan wani jami’inta ma suna Abdulgaffar Abiola.
Rundunar ta ce, Abdulgaffar ɗin yana tsare a wajenta inda take bincike a kansa kan karya dokar soja wajen amfani da kafafen sada zumunta.
Abdulgaffar dai yayi fice a kafafen sada zumunta da sunan “Cute Abiola” inda yake wasan barkwanci.
Sama da mutane miliyan biyu ne ke bin shafinsa na Facebook da a nan ne ya yi shuhura wajen fitar da faya-fayan bidiyon barkwanci.
Wannan dai na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin ruwan ta ƙasa Commodore Sulaiman Dahun ya aike wa Freedom Radio da safiyar yau Laraba.
Sanarwar ta gargaɗi jami’an sojin ruwa da su guji ke ta dokokin rundunar a yayin da suke gudanar da al’amuransu na rayuwa.
You must be logged in to post a comment Login