Ƙetare
Amurka ta bukaci Nijeriya ta kara inganta kayan aikin zabe gabanin zuwan na gwamnoni
Kasar Amurka ta yi kira ga hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya INEC da ta magance matsalolin da aka fuskanta na na’urar tantance masu kada kuri’a ta BVAS gabanin zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da za a yi ranar 11 ga watan Maris mai zuwa.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Ned Price, ce ta sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar.
Ta ce, ‘yan Najeriya na da hakki wajen samar musu da kayan aikin zabe mai inganci, wanda shi ne zai basu damar zaben shugaban da suke so ya mulke su’.
‘Haka kuma ta yi fatan hukumar INEC za ta sake inganta kayan aikin zabe kafin ranar zaben gwamnoni da ke tafe’.
Rahoton: Madeena Shehu Hausawa
You must be logged in to post a comment Login