Labarai
Amurka ta yaba wa Najeriya kan hanzarta yanke hukunci a shari’o’in ta’addanci

Amurka ta yaba da kokarin kasar nan kan yadda take hanzarta shari’o’in da suka shafi ta’addanci, bayan samun nasarar yankewa mutum 386 hukunci a wasu shari’o’i da aka gudanar a baya-bayan nan.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, babban mai ba da shawara na Amurka kan harkokin Larabawa da Afirka, Massad Boulos, ya ce kasarsa na maraba da wannan ci gaba, yana mai cewa hakan babbar alama ce ta karfafa gaskiya da adalci.
Ya kara da cewa wannan mataki na nuna yadda Najeriya ke kokarin tabbatar da hukunta masu laifi tare da inganta tsarin shari’a a yaki da ta’addanci.
You must be logged in to post a comment Login