Connect with us

Kiwon Lafiya

Amurka:Najeriya ce babbar jagorar ta a nahiyar Afrika

Published

on

Kasar Amurka ta bayyana Najeriya a matsayin jagorar nahiyar Afirka kuma babbar abokiyar huldar Amurka.

Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ne ya bayyana hakan lokacin da yake taya kasar murnan cikar shekaru 58 da samun ‘yancin daga Birtaniya.

Ya ce Najeriya ce jagorar Afirka la’akari da bunkasar harkokin Dimokradiyya da ci gaban tattalin arziki da ma samar da aikin yi ga al’ummar kasa.

Mike Pompeo ya bukaci Najeriya ta ci gaba da harkokin jagorancin ta hanyar shirya ingantaccen zabe kuma karbabbe a shekarar badi, inda ya ce Amurkar za ta ci gaba da tallafawa Najeriya don fadada komar tattalin arziki, zuba jari da kuma yaki da cin hanci da rashawa.

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!