Labarai
An ƙaddamar da shirin ƙidayar yara da mata
Hukumar kididdiga ta jihar Kano ta kaddamar da shirin samar da bayanai na yara ‘yan kasa da shekaru 5 da mata dake tsakanin shekarun haihuwa.
Shugaban hukumar Malam Baballe Ammani, ne ya shaida hakan, yayin kaddamar da shirin na MIC 6.
Yace shirin wanda hadaka ne da sauran Kungiyoyin tallafi na duniya, zai maida hankali ne wajen kula da bayanan walwalar mata da sauran bukatun su, tare da kananan yara dake samun rigakafin cututtuka.
Da take jawabi tun da fari, shugabar shirin na MICS/NICS Abiola Arosanye, ta bayyana cewa shirin zai kwashe tsawon watanni uku ana gudanar da shi.
Ta kara da cewa shirin zai maida hankali wajen samar da bayanan al’umma da matsalolin da suke fuskanta ga Gwamnati, don daukar matakan da suka kamata.
You must be logged in to post a comment Login