Labarai
An fara binciken wadanda suke da hannu a asarar hannayen jari da Najeriya ta yi
Gwamnatin tarayya ta fara gudanar da tambayoyi ga mutanen da ake zargi suna da hannu cikin wata badakala wanda ta yi sanadiyar al’ummar kasar nan dubu sittin da biyar su ka yi asarar hannayen jari da suka zuba cikin wani kamfani da ya kai dala biliyan biyu
Wadana aka gayyata Kason farko don yi musu tambayoyi sun hada da: tsohon Ministan kasafin kudi da tsare-tsare Sanata Udoma Udo Udoma da takwaransa na kasuwanci da zuba jari Okechukwu Enelamah.
Lauyan wadanda suka fallasa badakalar da ya janyo asarar Chukwuemeka Obasi shi ya bayyana haka ga manema labarai jiya a Abuja.
A cewar sa jami’an tsaro sun kuma yi tambayoyi ga manajan daraktan bankin Union Emeka Emuwa wand shi ana zargin yana da hannu wajen faruwar lamarin.
Mr Chukwuemeka Obasi ya kuma ce duk wani kamfani ma zaman kansa da hukumomi da cibiyoyin gwamnati da ke da hannu cikin lamarin tuni sun gurfana don amsa tambayoyi