Labarai
An bayyana kasashen da Nijeriya za ta kara da su a gasar matasa ‘yan kasa da shekaru 23.
Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya ta matasa ‘yan kasa da shekaru 23 za ta kara da kasar Afrika ta kudu da Zambia da Cote d’Ivoire a rukunin B a gasar cin kofin Afrika ta matasa ‘yan kasa da shekaru 23 na shekarar bana.
Mai masukin baki kasar Masar ta fada a rukunin A wanda ke kunshe da kasashen Ghana da Cameroon da kuma kasar Mali.
A jiya Laraba ne aka fitar da rukunan gasar a birinin Alexandria dake kasar Masar wadda zata gudana daga ranar 9 ga watan nuwamba zuwa ranar 22 ga watan na nuwamba.
Za fafata wasannin ne a filayen wasa guda 2, wato babban filin wasa na Cairo da filin wasa na Al Salam Stadium
Nigeria dai ita ce mai rike da kambun gasar bayan da ta lashe a shekarar a 2015.
Kungiyoyi uku da suka samu nasara a gasar sune zasu wakilci nahiyar Afrika a gasar gasar cin kofin duniya ta matasa ‘yan kasa da shekaru 23 wadda zata gudana a birnin Tokyo na kasar Japan a shekarar 2020.