Labarai
An bude gadar Lado bayan hatsarin da Tirela ta yi a kafar hawan ta
Al’amura sun koma dai-dai a kan gadar Ado Bayero da ke daura da asibitin koyarwa na Aminu Kano, wadda aka fi sa ni da gadar Lado, bayan da aka rufe ta a daren jiya Litinin sakamakon wani hatsarin da babbar motatar daukar kaya ta yi a kafar hawa gadar.
Babbar dai ta yi awon gaba ne da karfen da aka sanya domin hana manyan motoci bi ta kan gadar lamarin da ya janyo sanadiyyar lalacewar karfe tare da haddasa cunkoso.
Direban babbar motar Abdulhamid Ayuba, a zantawarsa da Freedom Radio ya ce, birkin motar ne ya shanye a dai-dai lokacin da ya tunkarar gadar.
Haka kuma ya kara da cewa kasancewar wurin da ya kamata ya bi watau kasan gadar akwai cunkoson ababen hawa, don haka ya ga gwara ya tunkari saman gadar wanda babu kowa a wurin.
Direban wanda ya ce, hatsari ya faru ne a hanyarsa ta zuwa shan mai, ya kuma ce Allah ya kare don kuwa babu wanda ya samu rauni sakamakon hatsarin.
A nasa bangaren tun lokacin afkuwar hatsarin mai magana da yawun hukumar KAROTA Nabulisi Abubakar Kofar Na’isa shi ne mai magana da yawun hukumar KAROTA ya ce, tuni suka nemi agajin masu ruwa da tsaki don ganin an samar da mafita dangane da ifila’in.
You must be logged in to post a comment Login