Coronavirus
An bude sabuwar cibiyar gwajin Corona da Dangote ya samarwa Kano
Gidauniyar Aliko Dangote ta damkawa gwamnatin Kano cibiyar gwajin cutar Corona ta tafi da gidanka da ta samar a asibitin Muhammadu Buhari dake Giginyu.
Cibiyar gwajin za ta rika gwada mutane 400 a kullum, sannan bayan mako daya ta gwada mutum 1000 a rana.
A yayin taron mika cibiyar gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya godewa Alhaji Aliko Dangote bisa ga wannan al’amari na wannan namijin kokari da yayi.
A nata bangren Dakta Zuwaira Yusuf wacce itace shugabar gidauniyar Dangote tace sunyi wannan taimakon ga Kano ne duba da irin samun karin masu cutar da ake samu a Kano.
Da yake jawabi shugaban tawagar likitoci da aka turo Kano daga gwamnatin tarayya Dakta Nasir Sani Gwarzo ya ce an fara bincike domin gano abinda ya jawo yawaitar mace-mace a Kano.
Wakiliyar mu Zahra’u Nasir ta rawaito cewa daga cikin masu taron sun hada da shugaban cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta Kasa NCDC Chikwe Ihekuezo.
You must be logged in to post a comment Login