Labarai
An bukaci makiyaya da ke zaune a kudancin Najeriya su koma Arewa
Kungiyar dattawar arewa ta Northern Elders Forum da takwararta ta, gamayyar kungiyoyin kishin al’umma ta arewacin kasar nan, sun bukaci Fulani makiyaya da ke da zama a kudancin kasar nan, da su gaggauta kwashe ya nasu ya nasu su dawo yankin arewa domin tsira da dukiyoyin su da kuma rayukansu.
A cewar gammayyar kungiyoyin na arewa, ci gaba da kada gangar yaki da al’ummomin kudancin kasar nan ke yi ga makiyaya, babu abinda zai haifar sai kara ta’azzara rashin fahimta tsakanin al’ummar Najeriya.
Da ya ke gabatar da jawabi ga gammayyar kungiyoyin wanda ya samu halartar matasan arewacin kasar nan da dama, shugaban kungiyar ta Northern Elders Forum, Farfesa Ango Abdullahi, cewa ya yi, arewa ba za ta lamunci ci gaba da cin zarafin Fulani makiyaya ba, a don haka, ya ce, gamayyar kungiyoyin suka ga dacewar Fulani makiyaya, su bar yankin na kudanci.
Farfesa Ango Abdullahi, ya kara da cewa, la’akari da irin zafafan kalamai da gwamnonin kudanci ke furtawa abaya-bayan nan kan Fulani Makiyaya, yana nuna cewa ke nan, rayuka da dukiyoyin makiyaya na cikin hatsari.
Da ya ke gabatar da jawabi jagoran gamayyar kungiyoyin kishin al’umma a arewa, Abdul’aziz Sulaiman, wanda ya gabatar da bukatar kungiyoyin ga majalisar dattawa ta arewa, ya ce, a ranar tara ga watan nan gwamnonin kudancin kasar nan sun yi taro sun kuma cimma matsaya kan cewa, za su dakile zirga-zirgar Fulani makiyaya a yankunan su.