Kaduna
An dakatar da ƴan majalisa uku a Kaduna
Majalisar dokokin jihar Kaduna, ta dakatar da tsohon mataimakin shugaban majalisar Muktar Isa Hazo da wasu ƴan majalisa biyu har tsawon wata tara.
Dakatarwar ta biyo bayan karɓar rahoton kwamitin ɗa’a na majalisar a Talatar nan.
Kwamitin ya zargi ɗan majalisa mai wakiltar Kagarko Nuhu Goro da Yusuf Liman dake wakiltar Maƙera da kuma Muktar Isa Hazo dake wakiltar Basawa da yunƙurin juyin mulki a majalisar.
Haka kuma kwamitin ya buƙaci wasu ƴan majalisar biyar da a baya aka zarga da shiga cikin wannan juyin mulki da su rubuta takardar baiwa majalisar hakuri a shafukan manyan jaridun kasar a bisa laifin da suka aikata na kawo yamutsi a majalisar.
Ƴan majalisun da aka umarta da su bada hakurin, sun haɗa da tsohon shugaban majalisar Aminu Abdullahi Shagali da Salisu Isa da kuma Nasiru Usman.
Sai kuma Yusuf Salihu Kawo da kuma Abdulwahab Idris Ikra
You must be logged in to post a comment Login