Labarai
An dakatar da jirgin saman Emirates fita daga Najeriya – NCAA
Gwamnatin tarayya ta dakatar da kamfanin jirgin sama na Emirates daga fita Najeriya tsawon sa’o’i 72.
Hukumar kula da sufurin Jiragen sama ta Najeriya ce ta sanar da hukuncin.
Dakatarwar dai ta biyo bayan sabawa ka’idojin da kwamitin kar ta kwana mai yaki da cutar corona na shugaban kasa ta sanya don yaki da cutar.
Ana zargin kamfanin jirgin da dauko fasinjoji ba tare da yin gwajin cutar corona ba, a don haka hukumar ta dakatar da tashin jiragen daga filayen jirgin saman Murtala Mohammed da ke Lagos da kuma na Nnamdi Azikwe da ke Abuja.
You must be logged in to post a comment Login