Labarai
An dakatar da kasar Mali daga kungiyar ECOWAS
Kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afurka ta ECOWAS ta dakatar da kasar Mali daga ci gaba da kasancewa mamba a cikin kungiyar.
Ecowas ta ce ta dau wannan mataki ne a matsayin mai da martini ga juyin mulki da sojoji su ka yi ga shugaba Ibrahim Boubacar Keita
Bugu da kari kungiyar ta ECOWAS ta kuma sha alwashin sanya takunkumin karya tattalin arziki ga kasar.
A jiya talata ne dai sojoji a kasar ta Mali suka kama Ibrahim Boubacar Keita da firaministan kasar, Boubou Cisse tare da tursasa shi yin murabus.
A cikin wata sanarwa da kungiyar ta ECOWAS ta fitar a yau Talata, ta ce, za ta dauki matakin rufe kan iyakokin kasashe mambobin kungiyar ga kasar ta Mali sannan za ta bukaci daukar matakin sanya takunkumi kan shugabannin soji da suka gudanar da juyin mulkin.
You must be logged in to post a comment Login