Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

UEFA zata iya hana Neymar buga wasan karshe na champion leage

Published

on

Gwarzon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta PSG Neymar na fuskantar barazanar dakatarwa daga doka wasan karshe a gasar zakarun nahiyar Turai ta UEFA sakamakon canjin riga da yayi bayan da kungiyarsa tayi nasara a wasan kusa da na karshe da RB Leipzig.

Bayan da PSG tayi nasarar doke RB Leipzig da ci 3 da nema a kasar Portugal sai Neymar da dan wasan RB Leipzig Marcel Halstenberg su kayi masanyar riga.

A na dai tuhumar Neymar da take dokar cutar Corona, lamarin da ka iya sanyawa a hana dan wasan taka leda a wasan karshe a gasar.

Rahotanni na cewa, yayin da aka dawo cigaba da gasar ta UEFA daga hutun Corona, an saka dokar hana doka wasa daya ga dukkan dan wasan da aka samu da canjin riga yayin gudanar da wasa tare da killacesa har tsawon kwanaki 12.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!