Labaran Wasanni
An dakatar da wasan Tennis saboda barazanar cutar codiv 19.
Hukumar kwallon Tennis, ta duniya ITF, ta sanar da dage wasannin share fagen shiga gasar Fedaration cup, da wasan karshe na gasar sakamakon tsoron yaduwar cutar Coruna Virus.
Sanarwar ta fito ne kasa da mako daya, bayan da aka dage gasar Indian wells, da aka shirya gudanarwa a birnin California na kasar Amurka , bisa barazanar cutar wadda hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ayyana a matsayin annobar da ta mamayi duniya.
A wata sanarwa a shafin hukumar da shugaban hukumar Tennis ta duniya, ITF, David Haggerty, ya sakawa hannu ,yace sun dau matakin ne kasancewar gudanar da gasar zai iya zama hatsari duba da halin da ake ciki, don haka bayan shawartar gwamnatin kasar Hungary, wacce za’a gudanar da gasar a can, tare da hukumar Tennis ta kasar da ta mata, ya sa suka daga gasar, tare bada hakuri bisa afkuwar hakan.
Labarai masu alaka.
Cutar Corona ta sa an dakatar da ‘yan kallo shiga wajen wasanni
Cutar Coronavirus ta janyo faduwar danyan mai a Duniya
David Haggerty, ya kara dacewar hukumar na cigaba da tuntuba don samar da matsaya, da kuma lokacin da za’a gudanar da gasar a gaba in an samu kwanciyar hankali da lafawar cutar.
Wasannin dai an shirya gudanar da su ne a kasar ta Hungary, a ranakun 14 zuwa 19, a filin wasa na Laszlo Papp Sport Arena, a birnin Budapest, ya yinda kuma a za’a gudanar da wasannin cancanta a ranakun 17 da 18, na watan Afrilu a filayen wasanni guda takwas a kasar ta Hungary.
Gasar wacce zata zama tikitin samun shiga gasar wasannin bazara na Olympic, ta samu tasgaro inda hukumar ta ITF, tace zata yi aiki kafada daya da hukumar shirya gasar Olympic, IOC, don cimma matsaya akan ‘yan wasa da zasu halarci gasar wadda za ta gudana a birnin Tokyo na kasar Japan.
You must be logged in to post a comment Login